Labarai
Kano: Ƴan sanda sun cafke matasa 14 bisa zargin fashi da ƙwace wayoyi
Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta ce ta cafke wasu matasa su goma sha huɗu bisa zarginsu da aikata fashi da makami da tu’ammali da ƙwayoyi da harkokin daba har ma da ƙwace wayoyin salula a makon farko na watan Azumin Ramadan.
Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a Alhamis ɗin makonnan.
Ta cikin sanarwar, SP Kiyawa ya ce, rundunar ta samu nasarar cafke matasan ne a wani samame da kai na yunƙurin ta dawo da zaman lafiya.
Haka kuma ta ƙara da cewa ta samu ɓata garin da muggan maƙamai da miyagun ƙwayoyi da kuma kayayyakin da suka sata.
