Connect with us

Labarai

Kotu ta yi umarnin mayar da shugaban majalisar dokokin Filato da aka tsige

Babbar kotun jihar Filato da ke zamanta a Jos babban birnin jihar, ta bayar da umarnin dawo da Abok Ayuba a matsayin shugaban majalisar dokokin jihar Filato da aka tsige.

Kotun ta bada umarnin ne a zamanta na yau Litinin.

Alkalin kotun, Mai shari’a Nefisa Musa, wadda ta yanke hukuncin, ta amince da roko da karar da ya shigar a kotu.

Alkalin ta ce, tsarin da aka bi na cire Ayuba ya saba wa doka.

Aboka Ayuba, ya godewa jama’ar jihar Filato da suka taya shi jaje da jimami daga lokacin tsige shin har zuwa samun nasararsa.

“Har yanzu muna da sauran watanni da za mu ci gaba da yin aiki a mazabunmu ga al’ummar da suka zabe mu.

“Duk da cewa an yi rikici a wasu lokutan baya, amma a yau kotu ta ba da wadannan sharuddan na dawo da ni kasancewar abinda aka yi ya saba wa doka,” in ji shi.

Haka kuma, ya ce da yardar Allah zai ci gaba da aiki cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.

Ayuba ya ce ba zai yi fada da kowa ba, ya kara da cewa dukkansu ‘yan majalisar ne kuma duk ‘yan Filato ne kuma ‘yan Najeriya.

Idan za a iya tunawa ƴan majalisar dokokin jihar sun tsige Abok Ayuba ne a ranar 28 ga Oktoba, bara.

Sai dai tun a lokacin ya kalubalanci tsigewar tare da bayyana ta a matsayin abida ya saba wa ka’idar majalisar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino sitelerikavbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciograndpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet