Labarai
Daruruwan Fursinoni A Kano Sun Amfana Da Duba Lafiyarsu Kyauta
Daurarru sama da dubu daya ne dake zaune a gidajen gyaran hali na goron Dutse da Kurmawa a jihar Kano ne suka amfana da ganin likitoci daban daban tare da ba su magani kyauta.
Yayin wani aikin sa kai da nufin neman lada a wajan Allah da tawagar kungiyar likitoci musulmi suka yi karkashin jagarancin shugaban kwamitin gudanar da aikin Dr. Sule Abdullahi Gaya.
Shugaban kungiyar na jihar Kano Dr. Muhammad Auwal yace suna yin aikin ne dan taimakawa marasa karfi a wurare daban daban, tare da basu kayan abinci da ruwa, da makamantan su.
A jawaban su daban daban Dr. Anas Ibrahim Yahaya Bichi da Dr. Muhammad Lawan Adamu wadanda suna cikin likitocin da suka duba marasa lafiyar da dama, sun bayyana cewa cikin tawagar su ta Likitocin babu irin likitan da babu, dan haka kowacce irin cuta suka ci karo da ita sun tanadi maganin ta.
Daga bisani mai kula da gidan gyaran halin na Kurmawa DC Mu’azu Tukur wanda ya yi jawabi a madadin shugaban hukumar ya nuna godiya da jin dadin su kan aikin da kungiyar likitoci musulmi suka yi ga daurarrun.
