Labarai
Hukumar Kashe Gobara Ta Ceto Rayuka 45 Da Miliyoyin Dukiya A Kano
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ceci rayuka 45 da dukiyoyin da kudinsu ya kai Naira miliyan 285.6 a cikin gobara 86 da ta afku a watan Maris, kamar yadda kakakinta, Alhaji Saminu Abdullahi ya bayyana a ranar Litinin.
Ya kara da cewa, mutane 11 ne suka rasa rayukansu yayin da gobarar ta lalata dukiyoyin da ta kai Naira miliyan 113.2 a lamarin.
Sanarwar ta ce hukumar ta amsa kiran ceto 43 da kuma na karya guda 10 daga mazauna jihar cikin wannan lokacin. (NAN)
