Addini
2023: Hukumar Alhazai NAHCON Ta Sanar Da Farashin Aikin Hajjin Bana
Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta ce kowane maniyyacin aikin hajjin shekarar 2023 zai biya mafi karancin Naira miliyan 2.89.
Shugaban Hukumar NAHCON, Zikrullah Hassan ne ya sanar da hakan a ranar Juma’ar nan a Abuja.
Hassan ya danganta karuwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya da Saudiyya.
Ya ce an tsayar da sabon farashin kudin ne bayan tattaunawa da shugabannin hukumar alhazai ta jiha.
Ya ce farashin ya kai nau’i 8 tare da jihohin Borno da Adamawa don biyan mafi karancin farashi yayin da Jihohin Legas, Ogun da Oyo mafi girma da Naira miliyan 2.99.
Shugaban ya ce shugaban kasa Muhammad Buhari ya kuma amince da kamfanonin jiragen sama don jigilar maniyyatan Najeriya zuwa aikin Hajji.
Ya kara da cewa ranar 21 ga watan Afrilu, 2023 ita ce ranar karshe na aikawa da kudade ga hanyar masu niyyar aikin Hajjin.
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Hakazalika, Shugaban ya kara da cewa a ranar 21 ga watan Mayu ne za a fara jigilar mahajjatan bana.
