Addini
Hukumar NAHCON ta sanya kusan Naira Miliyan 3 a matsayin kuɗin Hajjin Bana
Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya NAHCON, ta ce, a bana maniyyata aikin hajjin za su biya Naira miliyan biyu da dubu ɗari takwas da casa’in a matsayin kuɗin kowacce kujera guda.
Shugaban hukumar Zikrullah Hassan, ne ya bayyan hakan yau Juma’a, yana mai cewa matsalar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya da Saudiyya ne suka janyo ƙaruwar kuɗin Hajjin a bana.
Haka kuma ya ce, farashin ya kai matakai takwas, inda jihohin Borno da Yobe suka kasance jihohi da za su biya kuɗi mafi ƙaranci, yayin da jihohin Lagos da Ogun za su biya kuɗi mafi yawa da ya kai naira miliyan biyu da dubu ɗari tara da casa’in.
Ya ce, hakan ta kasance ne bisa bambancin kuɗin jirgi da kuma na masaukai a birnin Makka.
Shugaban hukumar ta NAHCON, ya ƙara da cewa, maniyyatan jihohin Arewacin Najeriya za su biya naira miliyan biyu da dubu dari tara da goma sha tara.
Jihohin Kudancin Najeriya kuwa za su biya kusan naira miliyan uku.
Zikrullah Hassan, ya ƙara da cewa, kamfanonin jiragen sama da aka amince su yi jigilar maniyyata sun haɗa da Air Peace da Azman da Fly Nas da Aero Contractors da kuma Max Air yayin da Arik Air da Value jet aka amince da su a matsayin jiragen haya masu zaman kansu.
