Connect with us

Labarai

Kotu Ta Sake Aikewa Da Mawaki Dauda Rarara Takardar Sammaci

 

Babbar kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a unguwar Rijiyar Zaki a jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Halhalatul Khuza’i Zakariyya , ta yi umarnin a sake rubuta wa Dauda Abdullahi Adamu Kahutu ( Rarara) sabuwar sammaci sakamakon rashin halattar zaman kotun da yaƙi yi.

Ana ƙarar Dauda Rarara ne kan ƙin biyan wasu kuɗaɗen cinikayyar wayoyin Salula da yake karɓa yana raba wa mutane, a wajen wani Ɗan kasuwa mai suna Muhammad Ma’aji kimanin Naira miliyan goma da dubu ɗari uku.

Lauyan mai ƙara Barista I. Imam ya shaida wa kotun cewa, wanda ake ƙarar bai mutunta sammacin da aka kai masa ba , dan kuwa bai halacci zaman kotun ba.

Lauyan mai ƙarar ya roƙi kotun da ta yi umarnin a kamo Rarara kasancewar ya raina kotun.

Barista I. Imam ya ƙara da cewa bai san ko sammacin da aka ba wa wanda ake ƙarar ko ya isa gareshi.

Kotun ta, tambayi jami’in kotun da ya kai sammacin wato Isma’il Zuhudu ko shin ya kai sammacen?

Isma’il Zuhudu ya bayyana cewa haƙiƙa ya liƙe masa takaddar sammacin a Ƙofar gidan kamar yadda kotun ta yi umarni, sakamakon sun neme shi dan a bashi hannu da hannu amma ba a same shi ba.

Mai ƙarar Muhammad Ma’aji ya shaida wa manema labarai cewa ” cinikayya ce tsakanin sa da Rarara ta dogon lokaci kuma kuɗaɗen sun taru har yanzu bai bayar ba, wanda ya bi dukkanin matakan da suka kamata dan warware wa ,wanda hakan ya kai ga ya daina ɗaga wayarsa.

Kakakin manyan kotunan shari’ar addinin musulinci na jahar Kano Muzammil Ado Fagge, ya bayyana cewa , “daman an ta neman Rarara akan ƙarar da aka shigar amma ba a same shi ba , sai kotu ta yi amfani da Oda 3 sharaɗi na 5 (C) da a liƙe masa sammacin a ƙofar gidansa, kuma an liƙe masa kamar yadda kotu ta umar ta.

Mai shari’a Mallam Halhalatul Khuza’i Zakariyya, ya bayyana cewa kasancewar wanda ake tuhuma bai zo ba kuma bai aiko ba , kotun ta yi masa uzuri tunda dai wannan ne karon farko kuma kotun ta yi umarnin a sake rubuta sabon sammaci ga Dauda Rarara , a sake kai masa ko kuma liƙe masa a gidan sa dake gidan Zoo Kano tare da wallafa sammacin a shafukan sada zumunta da kafafan yaɗa labarai kotun ta sanya ranar Alhamis 13 ga watan Afrilu 2023 domin ci gaba da sauraran shari’ar .

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet