Connect with us

Labarai

Rashin Lafiyar Da Buhari Ya Yi Ta Cinye Watanni 8 Na Wa’adin Mulkinsa — Adesina

 

Babban mashawarci ga shugaban kasa Muhammadu Buhari bangaren yada labarai Femi Adesina ya ce rashin lafiyar shugaban kasan a shekarar 2017, wadda ta dauki tsawon watanni 8 na cikin waadin mulkinsa.

Adesina ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake magana a gidan Talabijin na Channels TV ta cikin shirin Politics Today, kamar yadda Dailystruggle ta rawaito.

Adesina wanda ke bayyana nasarori da gwamnatin Buhari ta samu a cikin shirin, ya ce shugaban ya shafe watanni takwas yana jinya a kasar Ingila a shekarar 2017.

“Lokacin da ya yi rashin lafiya a watan Janairun 2017, ya dawo a watan Maris, ya sake tafiya a watan Afrilu kuma bai dawo ba sai 19 ga Agusta.

“Game da watanni takwas, Wannan ciwon ya ɗauki watanni takwas a ofis. Tabbas, babu wanda zai so hakan sai dai abin da muke farin ciki shi ne ya zo lafiya, lafiyayye kuma fiye da yadda ya tafi.”

Sai dai ya ce duk da wannan koma-baya, shugaban zai bar kasar fiye da yadda ya gana da ita.

Adesina ya tuna cewa kananan hukumomi 17 na hannun ‘yan ta’adda a lokacin da Buhari ya karbi mulki a shekarar 2015, ya kara da cewa gwamnati ta kwato yankunan.

Ta fuskar tattalin arziki kuwa, ya yi nuni da cewa a yanzu Najeriya na da tattalin arziki iri daban-daban biyo bayan kokarin da gwamnatin Buhari ta yi, yana mai jaddada cewa “yanzu man fetur bai kai kashi 10% ba ga GDPn Najeriya.”

Kakakin fadar shugaban kasar ya kuma yi Allah wadai da sukar da limamin darikar Katolika na Sokoto, Matthew Kukah ya yi wa Buhari kan siyar da rundunar ta shugaban kasa.

Adesina ya bayar da hujjar cewa Buhari bai taba yin alkawarin sayar da jiragen shugaban kasa ba, yana mai cewa: “Wadancan abubuwan ba su yi wa Baba Kukah hankali ba. Wani mutum ne da a da dadewa muke sha’awar saninsa amma ra’ayinsa siyasa ce ta canza masa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet