Labarai
Aisha Binani ta garzaya Kotu
Ƴar takarar gwamnan jihar Adamawa a jam’iyyar APC, Sanata Aisha Binani, ta shigar da ƙara a kotu domin neman a bayyana ta a matsayin wadda ta lashe zaɓe.
Aisha Binani ta garzaya ne babbar kotu a Abuja inda ta shigar da ƙarar neman kotu ta dakatar da matakin da hukumar INEC ta ɗauka na soke bayyana ta a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamnan Adamawa bayan zaɓen da aka gudana ranar 18 ga watan Maris wanda kuma aka kammala ranar 15 ga watan nan da muke ciki na Afrilu.
Haka kuma ƴar takarar, ta buƙaci kotun ta hana INEC ɗaukar wani mataki na gaba dangane da bayyana wanda ya lashe zaɓen zuwa lokacin da kotu za ta saurari ƙarar da ta shigar.
Binani, Ta ce “Bayan da INEC ta bayyana ta a matsayin wadda ta lashe zaɓe, daga nan jam’iyyar PDP da ɗan takararta Gwamna Ahmadu Fintiri suka tada fitina wanda hakan ya yi sanadin aka lakaɗa wa wani jami’in INEC duka”.
Haka kuma ta bayyana cewa, hakan ne sanadin da ya sanya INEC soke bayyana nasararta da aka yi da farko, wanda a cewarta hukumar ba ta da hurumin yin haka face Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe.
Jaridar Blueprint ta ruwaito cewa, Ƙarar da Binani ta shigar ta shafi hukumar INEC da kuma gwamnan Fintiri.
