Labarai
Ƴan bindiga sun sace Tsohon shugaban ƙungiyar lauyoyi
Rahotonni daga jihar Rivers sun bayyana cewa, wasu da ba a kai ga gano su ba, sun yi garkuwa da tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya NBA Okey Wali SAN.
Jaridar Blueprint, ta ruwaito cewa, ɓata garin sun yi garkuwa da shi ne yayin da suka kai wa tawagarsa da safiyar ranar Litinin a yankin ƙaramar hukumar Obio Akpor ta jihar Rivers
A nata ɓangaren, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Grace Iringe Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin .
Haka kuma, ta ce ƴan sanda na yin bakin ƙoƙarinsu don kuɓutar da shi cikin ƙoshin lafiya.
