Labarai
Da ɗumi-dumi: An ga jinjirin watan Shawwal a Saudiyya
Hukumomin ƙasar Saudiyya, sun sanar da ganin jinjirin watan Shawwal.
Rahotonni sun bayyana cewa an gano jinjirin watan ne a yau Alhamis.
BBC ta ruwaito cewa, mahukuntan sun ce, An ga watan ne a yankin Tumair na Saudiyya kamar yadda kwamitin duban wata na yankin ya bayyana.
Haka kuma, ta ruwaito cewa, hakan na nufin Saudiyya ta kammala yin azumin Ramadan na bana kenan na tsawon kwanaki 29.
Haka kuma ta ƙara da cewa hakan na nufin gobe Juma’a ita ranar ɗaya ga watan na Shawwal.
