Labarai
A Shekaru 8 Na Mulkin Ganduje Ya Yafewa Fursunoni Sama Da 4,000
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi afuwa ga fursunoni 4,013 a cikin shekaru takwas a duk fadin jihar Kano.
Hakazalika, ya ce gwamnatinsa ma, a cikin shekaru takwas, ta yanke hukuncin biyan tara da diyya ga fursunonin har naira Naira miliyan 4.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun babban sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan jihar Kano Hassan Musa Fagge a ranar Juma’a.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dakta Nasiru Gawuna, ya bayyana haka a lokacin da ya yi afuwa ga fursunoni 43 da suka aikata laifuffuka daban-daban da suka yi zaman gidan yari a yayin bikin karamar Sallah da aka yi a gidan yari na Goron Dutse.
Yayin da yake jaddada cewa ’yanci shi ne komai na rayuwar dan Adam, ya yi kira ga fursunonin da aka yi wa afuwa da su nuna kyawawan halaye a duk inda suka samu kansu a cikin al’umma.
Kwanturola hukumar kula gidan gyaran hali a jihar, Suleiman Inuwa, ya bayyana cewa matakin da gwamnatin jihar Kano ta bayar na sakin fursunonin na biyan tarar da diyya da kuma afuwa zai taimaka wajen rage cunkoso da kuma tabbatar da zaman lafiya a gidan.
Ya kuma yi kira ga sauran jihohi da su yi koyi da wannan mataki, sannan ya bukaci wadanda suka amfana da su kasance jakadu nagari na hukumar gyaran hali ta Najeriya ta yadda za su kasance masu bin doka da oda ta hanyar nuna kyawawan halaye.
A nasa bangaren, Abdullahi Rano, ya godewa gwamnan bisa yadda ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi na sakin fursunonin bisa shawarar hukumar kula da gidan gyara hali da kuma majalisar.
