Connect with us

Labarai

Daya Daga Cikin Mutane 85 Da Aka Sace A Zamfara Ta Tsere Daga Sansanin ‘Yan Bindiga

Mutum guda 1 daga cikin mutane 85 da aka yi garkuwa da su a kauyen Wanzamai da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, Zainab Abdullahi, ta tsere daga sansanin ‘yan bindigar inda ta koma gida.

Sauran 84 kuma har yanzu suna hannunsu.

Da yake zantawa da jaridar PUNCH ta wayar tarho da yammacin ranar Juma’a, wani dan asalin yankin, Abubakar Na’allah, ya ce Zainab ta tsere ne a daren Juma’ar kuma ta sake haduwa da iyayenta a kauyen.

Na’allah ya ce Zainab na daga cikin ‘yan matan da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su wadanda yan bindigar suka zaba domin su debo itacen dafa abincin wadanda abin ya shafa a sansanin ‘yan fashin.

Da yake bayyana yadda ta kubuta, ya ce, “Lokacin da Zainab da wasu ‘yan mata suka je dibar itace, ita (Zainab) ta yanke shawarar guduwa ta samu ta dawo gida.

Na’allah ya ce yarinyar tana cikin koshin lafiya duk da ta yi fari.

Ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ‘yan fashin suka ki sakin mutanen da suka sace duk da Naira miliyan uku da suka karba daga al’ummar Wanzamai.

Majiyad Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa ‘yan bindiga sun karbewa al’ummar Wanzamai zunzurutun kudi har Naira miliyan uku domin a sako mutane 85 da aka yi garkuwa da su, amma bayan sun karbi kudin sai suka dage sai a biya su karin kudi.

‘Yan fashin sun kuma dage cewa a janye sojojin da aka tura kauyen Wanzamai daga kauyen.

Sai dai kwamishinan tsaro na jihar DIG Mamman Tsafe (mai ritaya) ya shaidawa jaridar PUNCH cewa gwamnatin jihar ba za ta janye sojojin da ke wannan kauyen ba.

“Ba za mu janye jami’an soji ba komai matsin lamba daga ‘yan bindigar,” in ji shi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet