Labarai
Bazan Manta Da Gwamnan Ganduje Ba Har Tsawon Rayuwata — Sarkin Kano
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce ba zai iya mantawa da gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ba har tsawon rayuwarsa.
Mai martaba sarkin ya bayyyana haka a Lahadin Nan a ziyarar da ya Kai fadar gwamnatin Kano, yayin bikin sallah a hawan Nassarawa.
Bisa al’ada a duk ranar uku ga Sallah sarkin Kan Kai ziyarar Barka da Sallah ga gwamnan Kano, bisa rakiyar Hakimansa.
Ya Kuma Yi kira ga al’ummar jihar Kano da su bada hadin Kai da ya kamata a lokacin da za a gudanar da kidaya.
Mai martaba sarkin Kano ya Kuma yi wa gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje fatan alkhairi, wanda a cewarsa wannan ne lokaci na karshen da zai karbi bakuncinsa a matsayinsa na gwamnan Kano.
A nasa jawabin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta bakin Mataimakinsa Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya godewa sarkin da masarautar Kano bisa hadin kan da suke basu a koda yaushe.
