Labarai
Daliban Fasaha Sun Yi Barazanar Rufe Hanya Ko Buhari Ya Sanya Hannu Kan Daidaita HND/BSC Nan Da Mako 2
Kungiyar daliban kwalejojin kimiyya da fasaha ta kasa ta bukaci shugaban kasa, Muhammadu da ya yi kokarin kawo karshen sabanin da ke tsakanin babbar difuloma da na digiri na farko kafin barin sa mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Mataimakin shugaban ta NAPS na Kasa, Adeniji Temitope, a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Litinin din nan, ya ce ba labari bane cewa daliban Najeriya da daliban da suka kammala digiri na biyu “sun fuskanci matsaloli tun shekarun da suka gabata.”
Adeniji ya ce masu ruwa da tsaki a fannin ilimin kimiyyar kere-kere sun bukaci majalisar dokoki ta tara da ta amince da “Kudurin dokar hana Wariya Tsakanin Digiri na Farko da Babbar Diploma ta Kasa.”
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa a shekarar 2021 ne majalisar dattijai ta zartar da wani kudiri na neman a soke baraka tsakanin takardar shaidar HND da masu digiri na jami’a a kasar.
Dokar wadda Sanata Ayo Akinyelure ya gabatar, ta yi karatu na uku a zauren majalisar dattawan.
Shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da manyan makarantu da kuma TETFUND, Ahmad Kaita, ya gabatar da rahotonsa, sannan majalisar ta amince da dukkan wasu sharruda shida da aka gyara.
Shugaban kwamitin hadin gwiwa na kungiyar Malam Ibrahim Shekarau (na APC, daga Kano ta tsakiya) ya ce, ” kudirin zai soke tare da haramta wariya a tsakanin masu digiri na farko da kuma babbar difloma ta kasa don neman aiki a Najeriya, ko shakka babu zai ‘yantar da masu HND daga tabarbarewar da tabbatar da daidaiton kulawa da takwarorinsu na sauran manyan makarantu a Najeriya.”
NAPS ta yaba da ci gaban tana mai cewa majalisar ta tara ta yi aiki mai kyau ta hanyar zartas da kudurin amma dole sai shugaban kasa ya amince zai zama doka.
“Sashen NAPS ta ofishin mataimakin shugaban ku giyar ya amince da rufe dukkanin makarantun kimiyya, kwalejojin fasaha da kuma cibiyoyin hadin gwiwa da ke ba da lambar yabo ta HND a fadin Najeriya idan har shugaba Buhari bai sanya hannu kan dokar HND/BSC ba nan da kwanaki 14 masu zuwa,” in ji sanarwar.
