Connect with us

Labarai

Kaso 96 Cikin 100 Na Matan Da Suka Tsaya Takara A 2023 Sun Sha Kayi A Wajen Maza

 

Kashi 96 cikin 100 na matan da suka tsaya takara a mukamai daban-daban a zaben shekarar 2023 da ya gabata sun sha kashi a hannun takwarorinsu maza, inji wani rahoton Jaridar Daily Trust.

Kimanin mata 1,553 nemi mukamai a zaben shugaban kasa da na gwamnoni da na majalisun tarayya da na jihohi da aka gudanar a ranakun 25 ga watan Fabrairu da 18 ga watan Maris na wannan shekara.

A cikin jimillar ’yan takara 15,307 da suka fafata a karkashin jam’iyyun siyasa 18 da aka yi wa rajista a babban zaben shekarar 2023, maza sun samu 13,754, wanda ya nuna kashi 89.8 cikin 100 yayin da ‘yan takarar mata 1,553 suka samu kashi 10.1 cikin 100.

Binciken sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana ya nuna cewa mata 72 ne kawai aka zaba a matakin tarayya da jihohi, yayin da 1,487 suka fadi.

Wadannan alkalumman sun hada da jihohin Kebbi da Adamawa, inda aka sake gudanar da zaben a ranar 15 ga watan Afrilun.

Yayin da Kebbi ba ta da ‘yar takara a zaben da aka kammala, Aishatu Binani, ‘yar jam’iyyar (APC) a Adamawa ta sha kaye a hannun dan takarar PDP, Ahmadu Fintiri, wanda ke da Farfesa Kaletapwa Farauta, mace a matsayin mataimakiyarsa.

Jaridar Daily trust ta rawaito cewa Takaddar mata 72 ne da suka ci zabe ya nuna cewa bakwai daga cikinsu an zabe su a matsayin mataimakan gwamnoni; Dr Hadiza Balarabe (Kaduna), Josephine Piyo (Plateau), Dr Akon Eyakenyi (Akwa Ibom), Dr Ngozi Nma Odu (Rivers), Engr Noimot Salako Oyedele(Ogun), da Patricia Obila (Ebonyi) da kuma Professor Kaletapwa Farauta (Adamawa).

17 daga cikin matan sun samu shiga majalisar dokokin kasar, uku a majalisar dattawa da 14 a majalisar wakilai.

A Jihohi, jimillar mata 48 ne suka samu halartar majalisun dokokin jihohi daban-daban.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet