Labarai
Hukumar NSCDC Ta Tura Jami’ain Da Za Su Sanya Ido Kan Jarabawar UTME A Jihar Kano
Hukumar kula da kadarorin gwamnati da tsaron al’umma Civil Defence a jihar Kano, sun tura jami’ai 422 zuwa cibiyoyi 37 da aka ware don jarrabawar samun gurbi a manyan jami’o’i da ke gudana a jihar.
Kwamandan jihar, Mista Adamu Salihu, ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN a Kano ranar Laraba.
Ya bayyana cewa an tura jami’an wuraren da za a gudanar da jarrabawar domin sanya ido kan aikin da kuma samar da tsaro a wuraren da aka kebe.
A cewarsa, rundunar ta tura jami’anta biyu zuwa kowace cibiyoyi 37 da ke fadin jihar domin tabbatar da gudanar da atisayen ba tare da tangarda ba.
“Za a yi zaman jarabawa uku na tsawon kwanaki uku kuma a kowane zama mun tura jami’ai biyu don sanya ido kan aikin.”
Salihu ya ce rundunar ba ta samu wani rahoto mara kyau ba kawo yanzu.
A cewarsa, shirin ya zuwa yanzu ba shi da cikas; babu batun satar jarrabawa, ba mu kama ba kuma yanayin yana da kyau.
Wakilinmu, wanda ya ziyarci wasu cibiyoyi, ya lura cewa an fara tantance masu jarabawar da wuri tare da samun gogewa daban-daban a yayin gudanar da ita.
Wani mai kula da cibiyar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an magance wasu matsalolin nan take.
Ya bayyana cewa har yanzu shirin babu mata matsala.
Jaridar Alkiblah ta ruwaito cewa ana sa ran mutane miliyan 1.5 za su shiga wannan atisayen a fadin kasar, ta hanyar amfani da jimillar cibiyoyi 740 na duk wani gwajin da aka yi amfani da shi a kwamfuta.
