Connect with us

Uncategorized

Modric ba zai buga wasan da Madrid za ta kara da Man City ba

Dan wasan Real Madrid Luka Modric da akwai yuwuwar ba zai samu damar buga wasan karshe na Copa del Rey da kuma wasan farko na wasan kusa da na karshe a gasar zakarun Turai da kungiyar za ta kara da Manchester City ba, saboda jinyar rauni da ya tafi.

Real Madrid ta ce dan wasan na tsakiya, ya samu rauni sosai a bayan cinyarsa, don haka yana bukatar kulawa ta musamman daga likitoci.

Kungiyar ta kasar Spain za ta buga wasan karshe na Copa del Rey da Osasuna a ranar 6 ga watan Mayu kafin wasan farko na wasan dab da na kusa da na karshe da Man-City a ranar 9 ga Mayun.

Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti, ya ce Modric ya ji rauni ne a wasan da suka fafata da Girona a ranar Talata.

An sauya Modric ne bayan mintuna 63 da fara wasan da aka doke su da ci 4-2.

Real Madrid za ta buga wasannin lig da Almeria da Real Sociedad kafin wasan karshe na Copa del Rey.

Dangane da raunin da Modric ya samu, Ancelotti ya kara da cewa: “Muna jiran mu ga yadda ya ke samun sauki, amma bani da tabbas ko zai kai wasan karshe.

“Mu na fatan zai samu damar shiga tawagar da za su wakilci Real Madrid a sauran wasannin da suka rage, wadanda suke da muhimmanci,” in ji Ancelotti.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet