Labarai
Sabon Kwamishinan ƴan sandan Kano ya yi gargaɗi kan karɓar Rashawa
Sabon kwamishinan rundunar ƴan sandan jihar Kano Muhammad Usaini Gumel, ya gargaɗi jami’an rundunar da su kauce wa aikata laifukan cin hanci da rashawa.
Kwamishinan, ya bayyana hakan ne yau Talata yayin da yake zantawa da manema labarai bayan da ya fara aiki a matsayin sabon Kwamishina na Kano.
Haka kuma ya ƙara da cewa rundunar za ta ci gaba da yin amfani da sabbin dabaru na zamani wajen cafke duk wasu masu aikata muggan laifuka a fadin jihar Kano domin tabbatarda tsaro da zaman lafiya.
Ya kuma buƙaci haɗin kan sauran hukumomin tsaro da ƙungiyoyin al’umma da kuma ƴan sandan cikin al’umma da su ci gaba da bai wa rundunar haɗin kai domin magance matsalar taɓarɓarewar tsaro.
Sabon Kwamishinan ƴan sandan na Kano, ya kuma ce, ko kaɗan ba zai lamunci aikata duk wani abu da zai ɓata wa jami’an ƴan sanda suna ba.
