Labarai
Ganduje Ya Bayyana Wanda Zai Shugabanci Zauren Majalisar Dattawa Ta 10
Gwamnan jihar Kano mai barin gado Abdullahi Ganduje ya amince da tsohon ministan harkokin Neja Delta Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawan Najeriya.
Ganduje ya bayyana haka ne a Calabar, babban birnin jihar Cross River a ranar Alhamis yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa takwaransa na Kuros Riba, Farfesa Ben Ayade.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, Gwamnan Kano wanda ya samu rakiyar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ibrahim Gambari ya ce matakin nada Akpabio ya riga ya kammala.
Jaridar Alkiblah ta rawaito cewa Sai dai bai bayyana ko shawarar da shugabannin jam’iyyar APC suka yanke ba kenan.
“Shugaban majalisar dattawan tarayyar Najeriya zai fito daga kudu maso kudu kuma ba wani mutum bane illa tsohon gwamnan Akwa Ibom.
“Gwamnan da ba na kowa ba, ba wai karamin ministan bane da zai zama shugaban majalisar dattawa ba. Don haka mun yanke hakan.
“Ina ba ku tabbacin, muna jiran ranar da ta dace cewa zai zama shugaban majalisar dattawan Najeriya,” in ji Ganduje.
