Labarai
Sudan: Zango Na Biyu Na Yan Najeriya 130 Da Suka Makale Sun Iso Nigeria
‘Yan Najeriya 130 ne da suka makale suka isa Najeriya da tsakar ranar Juma’ar nan daga Port Sudan.
A daren Laraba ne rukunin farko na ‘yan Najeriya da aka kwaso daga kasar Masar suka isa gida Najeriya.
Wakilinmu ya gano cewa ‘yan Najeriya 130; Mata 128 da maza biyu, sune farkon wadanda aka kwashe daga Port Sudan kuma jirgin ya isa da karfe 3:22 na rana.
A wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafin Twitter a safiyar Juma’a, Jakadan Najeriya a Sudan, Safiu Olaniyan, ya ce an yi ta cece kice, yana mai nuna farin cikinsa da cewa wasu daliban za su iso Najeriya.
Olaniyan ya lura cewa gwamnatin tarayya ce ta shirya jigilar jirgin.
Ya ce, “Bari in taya ku murna saboda kasancewar ku na farko da aka kwashe daga Port Sudan zuwa Najeriya. Yana da wahala amma daga ƙarshe an samu dace, muna kan hanyarmu ta gida.
“Muna yin addu’a. Har yanzu muna nan. Wasu ‘yan’uwanku maza da mata suna nan. Ba da daɗewa ba, za su kasance tare da ku.
“Wannan shi ne tsarin da Gwamnatin Tarayya ta yi muku. Ku yaba da abin da gwamnati ta yi. Har yanzu muna da sauran tafiya. Ina muku fatan a tashi lafiya.”
Jaridar Punch ta rawaito cewa Babban sakataren ma’aikatar jin kai, Nasir Sani-Gwarzo, ya ce ‘yan Najeriya 1,700 ne suka makale a karkashin kulawar gwamnati suna jiran a dawo da su Najeriya.
