Labarai
Majalisar Wakilai Ta Bukaci INEC Ta Goge Bayanan Duk Wanda Bai Yi Zaben 2023 Ba
Majalisar wakilai ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta goge bayanan masu kada kuri’a da sukayi rijista, amma suka kasa fita domin kada kuri’a a zabuka biyun da suka gabata.
Majalisar ta yi wannan kiran ne a ranar Alhamis din da ta gabata bayan amincewa da kudirin da Leke Abejide ya gabatar, yana mai cewa hakan ne ya kamata duba da batu daya shafi alumma ai tsaye.
‘Yan majalisar sun yanke shawarar cewa duk wanda bai kada kuri’a ba a zabukan biyu da aka gudanar a ranakun 25 ga watan Fabrairu da 18 ga watan Maris baya-bayan nan, za a goge shi daga rajistar INEC.
Sun yanke shawarar cewa INEC ta samar da wata hanya ta karbar bayanai musamman daga iyalan wadanda sun yi rijistar a baya, amma yanzu kuma sun rasu, domin goge su daga rumbun adana bayanan hukumar.
To said ai hakan ya gamu da cikas tun a zauren majalisar, Da yake magana kan batun, Nicholas Ossai, ya ce shawarar ta saba wa ka’idar tsarin mulkin 1999. Ya ce ‘yancin kada kuri’a batu ne na daban, haka fita domin kada kuri’ar ma abun ne daban.
Mista Ossai ya bayyana cewa kudirin ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, inda ya kara da cewa “Zai tauye hakkin ‘yan Najeriya”.
To sai dai Sada Soli (APC, Katsina) ya ce kudirin na neman INEC ne kawai ta tsaftace rajistar ta gabanin zabukan da za a yi a jihohin Kogi, Bayelsa da kuma Imo.
