Connect with us

Ilimi

Gwamnatin Tarayya Ta Yabawa Hukumar Shirya JAMB

 

Gwamnatin tarayya ta yabawa hukumar shiryya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire ta JAMB.

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin da yake sanya ido tare da rijistaran hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, kan sauya ranar UTME a cibiyar jarabawar CBT da ke Barrack Mambila Asokoro, a Abuja.

Kimanin dalibai 80,000 ne, wadanda basu iya samun damar rubuta jarabawar UTME ta 2023 ba a cikin lokacin da aka kayyade ba tare da wani laifin su ba.

Gwamnatin tarayya ta yabawa hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire JAMB bisa yadda ta gudanar da jarabawar UTME 2023 cikin nasara.

Duk da cewa an fara gudanar da atisayen, Adamu ya ce ya gamsu da yadda aka gudanar da atisayen cikin tsari, inda ya ce ya ji dadin abin da ya gani a cibiyar.

Ya ce: “Na yi farin ciki da abin da na gani dangane da dakin jarabawar (na wucin gadi) (na ’yan takara), da tsare-tsare da suke gudanar da jarabawar, ina ganin komai yana cikin tsari.

“Komai lafiya, ka ga wata matsala? Watakila su sami ajin da zasu yi jarabawar, ina ganin wannan ne kawai ci gaban da za su yi a nan,” in ji Adamu.

A halin da ake ciki, shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar ta JAMB, Dakta Fabian Benjamin, a wata hira da aka yi da shi a ranar Asabar, ya ce kimanin ‘yan takara 80,000 ne, wadanda basu iya zana jarabawar UTME ta 2023 ba a cikin lokacin da aka kayyade ba tare da wani laifin sun ba.

“Sannan zasu zana jarabawar UTME da za’a sake yi a fadin kasar.

A cewar kakakin hukumar ta JAMB, ‘yan takarar da abin ya shafa sun hada da wadanda aka tantance a cibiyoyinsu amma ba su iya samun damar zana jarabawar ba, da wadanda ba a iya tantance su ba.

Ya ce tura sabbin bayanai wajen gudanar da jarabawar sun samu sakamako mai kyau yayin da aikin ya nuna mafi karancin rahoton da aka samu na cin zarafi.

Fabian ya ce “A cikin UTME na bana, an rage matsalar rashin aikin jarabawa zuwa kusan matakin sifili.”

Yayin da hukumar jarabawar za ta fitar da sakamakon jarabawar UTME da aka sake shiryawa, Benjamin ya ce hukumar gudanarwar za ta yi nazari kan yadda aka gudanar da atisayen bayan kammalawa kafin ta yanke shawara kan hakan.

Idan ba a manta ba JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa a ranar Talata ne hukumar ta fitar da sakamakon jarabawar da aka fara a ranar Talata 25 ga watan Afrilu.

Jimlar ‘yan takara 1,586,765 ne suka nuna sha’awar yin jarabawar UTME ta 2023.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet