Labarai
Jami’an Yan Sanda Sun Kama Mutane Sama Da 100 Bisa Wasy Zarge-zarge
Jami’an ‘yan sanda da ke gudanar da aikin bincike na yau da kullun, a jihar Delta sun samu nasarar kama wasu mutane Maza 59 mata 94, bisa zargin su da aikata laifukan baɗala.
Mutanen an kama su a wajen da suke gudanar da sana’ar karuwanci, a Evweri a yankin karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar Delta.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma samu nasarar kwato bindigogin da wuka daya, harsashi masu rai guda 10, da kuma Mota sauran wasu kayayyaki na daban a wajen mutanen.
Haka kuma an kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da mota kirar Peugeot mai lamba KJA 98 GE, hadi da kayan shaye shaye da dama, da suka haɗar da codeine da Wiwi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar labarin a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu kuma aka mika wa DAILY POST.
Ya ce: An gurfanar da mutanen 94 a gaban kotu tare da wasu mazan da ake zargin, yayin da wasu kuma aka mika su hedikwatar rundunar don ci gaba da bincike.
A cewar Edafe, sashen ayyuka na rundunar ‘yan sandan jihar Delta, SIB, Dragon Patrol, Safer Highway Patrol, Raiders, CP D-Coy Squad, da Rapid Response Squad, RRS ne suka yi kamen.
Wasu daga cikin wadanda ake zargin, sun tabbatar da cewa an kama su ne bisa sahihan rahotannin sirri bayan samamen da aka gano a yankin karamar hukumar Ughelli ta Arewa.
