Kannywood
Lokuta Da Dama Nakan Bi Ra’ayin ‘Ya’yana, Mai Makon Nawa — Ali Nuhu
Fitaccen Jarumin nan a masana’antar shirya fina finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu ya ce a lokuta da dama ya kan bi ra’ayin yayansa, maimakon ra’ayinsa akan su.
Yayin wata hira da BBC tayi da Jarumin, ya ce a burin da yake da shi, shine dansa ya zama magajinsa wato shima ya zama tauraro, amma kuma maimakon hakan sai dan nasa ya zabi bin wata hanyar ta daban.
Ya ce Dan sa mai suna Ahmad Dan shekaru 16 ya fi kaunar ya zama ɗan kwallo, yayin da yar sa macen Fatima ke da sha’awar karantar ilimi alakar kasashen duniya.
A cewarsa bai tausaya kowa daga cikin su hakkinsa ba, Maimaikon hakan ya basu dukkanin gudunmawar da suke da bukata domin Cikar burin su.
Wannan martani na Jarumi Ali Nuhu na a matsayin martani ga masu ganin cewa kalubale ne ga taurarin fina finan kin saka yayan su cikin harkokin su na Fim.
Dangane da masana’antar fina finan Hausa kuwa, Ali Nuhu ya ce an samu ci gaba sosai, a yadda masana’antar ke gudanar da ayyukan ta.
Ya ce zuwa shafukan zamani irin su Netflix da Amazon ta kara taimakawa wajen bunkasar harkar ta fim din Hausa cikin sauri.
