Featured
Zai yi wahala Kannywood ta maye gurbin Aminu S. Bono – Rarara
Fitaccen mawaƙin jam’iyyar APC Dauda Adamu Abdullahi wanda aka fi sani da Rarara, ya bayyana alhininsa kan rashin Daraktan Kannywood Aminu S. Bono.
A sanarwar da Rarara ya fitar ta hannun makusancinsa Malam Abdullahi Al-Hikima, ya bayyana irin kyawawan halayen da marigayin yake da su.
Rarara ya ce, ya kamata sauran jama’a su yi koyi da riƙo da addini da ƙaunar juna da son ci gaban al’umma kamar yadda marigayi S. Bono ke da shi.
Ya ƙara da cewa, za a jima ba a manta da gudunmawar marigayin ba, wajen ƙara haɓɓaka masana’antar Kannywood tare da tafiya da zamani.
Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin da sauran al’umma bakiɗaya, yana mai cewa rashin Aminu Bono na dukkan al’umma ne.
