Featured
Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da nasarar Abdullahi Sule a matsayin gwamnan Nassarawa
Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da nasarar zaɓen gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa.
A hukuncin da kotun ta yanke yau Alhamis, alƙalan kotun sun bayyana cewa, kotun sauraron ƙorafin zaɓen gwamnan jihar Nasarawa ta yi kuskure a hukuncin da ta yanke.
A watan da ya gabata ne dai kotun sauraron ƙorafin zaɓen jihar Nassarawa ta soke nasarar gwamna Abdullahi Sule na jam’iyyar APC, tare da bayyana David Ombugadu na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen na watan Maris ɗin 2023.
Tun farko, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC, a sakamakon zaɓen gwamnan jihar ta ce Abdullahi Sule na APC ya samu ƙuri’a 347,209, inda ta ce ya doke Ombugadu na PDP, wanda ya samu ƙuri’a 283,016.
