Labarai
Kano: Matasa fiye da 10 sun mutu sakamakon shan Shayi mai Zaƙami
Mazauna unguwar sheka a yankin karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano, sun shiga halin zullumi sakamakon mutuwar fiye da matasan yankin 12 bisa shan wani shayi mai dauke da sinadarin Zakami.
Rahotonni sun bayyana cewa, a karshen makon da muka yi bankwana da shi ne matasan suka gamu da ajalin nasu a wani gida da ake gudanar da bikin Daurin aure.
Sai dai tuni Angon bikin ya arce inda har kawo yau Laraba ake ci gaba da nemansa Ruwa a Jallo.
A ganawar wasu daga cikin iyayen matasan da suka rasu, Malam Abdullahi Mahmud da Malama Hajara Abdullahi, sun bukaci da a hukunta duk wanda ke da hannu cikin lamarin kasancewar ‘ya’yan nasu sun sha shayin ne cikin rashin sanin an sanya sinadarin.
