Addini
Kotu Ta Tasa Ƙeyar Dr. Idris Kan Zargin Kalaman Batanci Ga Manzon Allah
Kotu ta tasa Ƙeyar malamin nan, Dr. Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi gidan yari bisa zargin furta kalaman rashin da’a ga Annabi Muhammad (SAW) da kuma kalaman ta da zaune tsaye.
Malamin wanda ya amsa gayyatar ‘yansanda a ranar Litinin, daga bisani sun gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin kalaman rashin da’a da ka iya barazana ga zaman lafiya.
Bayanan da ke zuwa mana na cewa ‘yansandan sun gurfanar da shi ne a gaban kotun Majistire ta 1.
Idan za a tuna dai furucin Malamin ya tayar da ƙura sosai ba ma a Jihar Bauchi ba a duk faɗin Nijeriya saboda abin da ya ambata wadda yanuna Babu girmamawa ga manzon Allah
