Labarai
Matasa sun Kona Babur na masu kwacan Waya
Ayanzu haka dai a iya cewa kora takai bango ga Al’ummar Johar Kano inda suka fara daukar doka a hannun su
A cikin daren ranar Asabar wasu fusatattun matasa sun yi dirar mikiya kan ƴan fashin wayar a unguwar Kabuga dake Kano, har suka ƙone Baburin adaidaita sahu ɗaya.
Ana zargin ƴan fashin wayar da yunƙurin aikata laifin, inda matasan da za a yi wa fashin wayar suka nemi taimakon jama’a.
Sai dai waɗanda ake zargin dukansu , sun gudu tare da barin adaidaita sahun da suke aikata laifin fashin wayoyin jama’a da kuma chaka mu su wuƙaƙe wanda hakan wasu ke rasa rayukansu
Yanzu haka dai an ƙone Baburin adaidaita sahun ƙurmus akan titin Kabuga kusa da layin yan Azara a jahar Kano.
Wannan na ɗaya daga cikin matakan da al’ummar jahar suka fara dauka na yin fito na fito na masu aikata laifin fashin wayar ɗauke da makamai masu Tsini.
Ko Akwanakin baya Saida Al’ummar yanki sukabi Wani matashi dayayi satar wayar yagudu zuwa cikin Wani bank kasuwanci Dan Neman tsira ,
wannan dabi’a tadade tana ciwa mutanan yankin tuwo akwarya , Tunga kabuga har zuwa unguwar Janbulo da rijiyar zaki
