Connect with us

Labarai

An ci kamfanin META tarar fiye da Yuro Miliyan 1,000

Rahotonni sun tabbatar da cewa, an ci kamfanin fasaha na Meta, ma mallakin shafikan sada zumunta na Facebook da Instagram da kuma WhatsApp tarar fiye da Yuro Miliyan 1,000.

An dai ci kamfanin wannan tara ne sakamakon musayar bayanai daga Turai zuwa Amurka ba bisa ƙa’ida ba kamar yadda kafar yaɗa labarai ta BBC ta wallafa.

Haka kuma ta ruwaito cewa, Kamfanin na fuskanatar tuhumar karya dokokin kare bayanan jama’a na Tarayyar Turai.

Wannan ita ce tara mafi girma da aka taba yi a karkashin dokar kare bayanan jama’a ta Turai, wadda hukumar Ireland ita ce ta yi wa kamfanin.

Bayanai sun ce an umarci kamfanin na Meta ya dakatar da aika sakonnin har tsawon watanni.

Shi kuwa ya ce zai daukaka kara kan tarar, inda kakakins Sir Nick Clegg ya ce za su bi hanyoyin shari`ar da sauran kamfanoni suke bi.

Hukumar tarayyara Turai ta yi dokokin ne domin tabbatar da kare bayanan jama’a idan za a fitar da su daga Turai.

To sai dai ana fargabar cewa wadannan bayanai ba lalle ba ne su samu kariyar da ta dace a Amurka wadda ke da raunanan dokokin kare bayanan jama’a, kuma hukumomin leken asiri na Amurka za su iya samunsu.

A baya Kamfanin ya yi barazanar dakatar da ayyukansa a Turai idan ba su cimma yarjejeniyar aike sakonni cikin sauki ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet