Labarai
Gwamna Ganduje ya rushe majalisar zartarwarsa
Gwamnan jihar kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bai wa ɗaukacin Kwamishinoni da shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnatinsa umarnin sauka daga mukamansu zuwa ranar Juma’ar makon nan da muke ciki.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babbar sakatariyar ofishin Bilkisu Shehu Maimota ta fitar a daren Litinin ɗin makon nan.

Sanarwar ta kuma bukaci masu mukaman Siyasa da su mika ragamar ma’aikatunsu ga manyan Sakatarorin gwamnatin ko daraktoci ma’aikatunsu tare da kayan gwamnati dake wurinsu.
”Wadanda aka bai wa mukami yana da wa’adin sauka to su cigaba da rike mukamansu dai-dai da yadda dokokin suka tanadar”. A cewar sanarwar
Sanarwar daganan ta godewa daukacin wadanda suka rike mukaman bisa ga irin gudunmawar da suka baiwa gwamnati da kuma irin nasarorin da aka samu tsawon shekaru 8 da suka gabata.
