Labarai
Shugaba Buhari ya rantsar da sababbin kwamishinoni 5
Yayin da ya rage kwana biyar ya sauka daga mulki, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya rantsar da sababbin kwamishinoni su biyar, da za su yi aiki a hukumar Tsara albashi RMAFC.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, shugaba Buhari, ya bai wa sabbin Kwamishinonin rantsuwar kama aiki ne gabanin fara gudanar da taron Majalisar zartaswa ta ƙarshe a gwamnatinsa yau ranar Laraba.
Haka kuma ta ruwaito cewa, Kwamishinonin sun haɗa da: Hawa Aliyu daga Jihar Jigawa da Rekiya Haruna Kebbi da Ismaila Agaka Kwara da Sanata Ayogu Eze Enugu da kuma Peter Opara Imo.
Sai kuma Kolawole Abimbola daga Jihar Oyo, da Ayuba Ngako daga yankin babban birnin tarayya.
