Labarai
Ƴan bindiga sun kashe basarake tare da ƙone gawarsa
Wasu da ake kyautata zaton cewa ƴan bindiga ne, sun hallaka babban basaraken garin Orsu Obodo da ke yankin ƙaramar hukumar Oguta ta jihar Imo, Eze Victor Ijioma da kuma wazirin garin Mgbele.
Rahotanni sun bayyana cewa ɓata garin, sun kashe shugabannin gargajiyar ne a hare-hare daban-daban jiya Alhamis.
Kafar Solacebase ta rawaito cewa, ƴan bindigar da ba a kai ga gano su ba sun hallaka babban basaraken ne a motarsa a garin Izombo kuma suka banka masa wuta.
Haka kuma, ta ruwaito cewa jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Juma’a.
