Labarai
Jirgin Nigeria Air ya yi lodi daga Addis Ababa zuwa Abuja
Jirgin farko na kamfanin jiragen sama na Nigeria Air, yana hanyarsa ta zuwa Abuja daga birnin Addis Ababa na ƙasar Ethiopia.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, da safiyar yau Juma’a ne jirgin na Nigeria Air ya fara lodi daga Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha zuwa birnin tarayya Abuja.
Haka kuma ta ruwaito cewa, ƴan Najeriya dai sun sha cewa sun gaji da gafara sa, ba su ga kaho ba, kan batun fara sifurin jirgin.
