Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta sanar da shirinta na yin gwanjon gidaje da filayen da ta ƙwace daga hannun masu almundahana.
A Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce, gidaje da filayen da za ta yi gwanjon suna biranen Abuja da Lagos da kuma wasu jihohin.
Haka kuma hukumar, ta wallafa ƙa’idoji da sharuɗan gwajon ga masu buƙata.
