Labarai
Gwamna Ganduje zai miƙa mulki yau Lahadi domin halartar rantsar da Tinubu
Gwamnan jihar Kano mai barin gado Dakta Abdullahi Ganduje, zai miƙa ragamar mulki ga sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Engr Abba Kabir Yusuf, yau Lahadi.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da kwamishinan labarai da harkokin cikin gida Malam Muhammad Garba, ya fitar yau Lahadi.
Malam Muhammad Garba ta cikin sanarwar ya ce, ana sa ran taron miƙa mulkin zai gudana da misalin ƙarfe 9:00 na daren yau a fadar gwamnatin Kano.
Ya ƙara da cewa, kwamitin miƙa mulki na gwamnatin jihar ta sanar da ci gaban ga kwamitin batun miƙa mulkin.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, bayan kammala taron Gwamna Ganduje zai tafi birnin tarayya Abuja a matsayin shugaban tawagar Kano zuwa bikin rantsar da sabon zaɓaɓɓen shugaban kasa Bola Tinubu a gobe Litinin.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, tafiyar gwamnan ta zama wajibi ne domin yin dai-dai da wa’adin rufe filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja domin bikin rantsar da sabon shugaban.
