Labarai
Gwamnatin Ganduje ta ayyana ƙwacen Waya a matsayin Fashi da makami
Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta ayyana ƙwacen wayar Salula a matsayin laifin da ya yi dai-dai da aikata fashi da makami.
Haka kuma, gwamnatin ta ce, daga yau Lahadi, duk wanda aka kama da aikata laifin za a yi masa hukunci iri ɗaya da na ƴan fashi.
Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Ta cikin sanarwar, Kwamishinan ya ce, ɗaukar matakin ya biyo bayan taron majalisar tsaro ta jihar Kano a zamantan na bankwana, wadda gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranta.
Ya ce, yawan faruwar ta’addar ƙwacen waya a jihar a ƴan kwanakin nan abin damuwa ne matuƙa wanda kuma ake buƙatar tsatstsauran mataki kafin a iya magance wannan matsala.
Malam Muhammad Garba ya ƙara da cewa majalisar ta amince da kafa wata runduna ta musamman a cikin jami’an tsaro da za ta riƙa yin yaƙi da mummunar ta’ada.
