Babban bankin Najeriya CBN, ya musanta wani rahoto da ke cewa ya karya darajar Naira ta koma 630 a kan duk Dalar Amurka ɗaya.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da muƙaddashin Daraktan sadarwa na CBN , Isa Abdulmumin, ya fitar ta ce, ko a jiya Laraba an sauya Dalar a kan Naira 465.
Sanarwar ta kuma ce, rahoton da wata jarida fitar ya bayyana cewa, rahoton ba na gaskiya ba ne.
Haka kuma Daraktan ta cikin sanarwar, ya jaddada matsayar babban bankin a kan lamarin inda ya ce ko a safiyar yau Alhamis an sauya naira 465 a kan Dala guda.