Labarai
Yadda Wasu Yan Majalisa Suka Ki Halartar Ganawar Tinubu Da Gwamnoni
Yayin da lokaci yake kara kusantowa da taron kaddamar da majalisar wakilai ta 10, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da zababbun Sanatoci na jam’iyyar APC, zababbun mambobin jam’iyyar APC, gwamnonin APC da shugabannin jam’iyyar kan batutuwan da suka shafi zaben shugabanni.
An gudanar da taron ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja a daren Laraba bayan kammala taron majalisar wakilai ta 9 da safiyar yau.
Masu neman kujerar kakakin majalisar, Muktar Betara, Yusuf Adamu Gagdi, Miriam Onuoha da Sada Soli sun halarci taron.
Sai dai mataimakin shugaban majalisar, Ahmed Idris Wase da Aminu Sani Jaji wadanda suma ke neman kujerar ba su je ba duk da an gayyace su zuwa taron.
An tattaro cewa shugaban kasar ya roki ‘yan majalisar da su marawa ‘yan takarar da jam’iyyar sa ta amince da su a matsayin shugabanci a majalisar dattawa da ta wakilai.
Ya yi magana kan bukatar ‘yan majalisar APC su yi aiki domin samun nasarar ‘yan takarar jam’iyyar APC na shugabancin NASS na 10.
