Labarai
Da na haɗu da Kwankwaso a Villa da na kauɗa masa mari- Ganduje
Tsohon gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce, idan da ya haɗu madugun Kwankwasiyya kuma jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a fadar mulkibta Villa da sai ya gaura masa mari.
Wannan dai ya biyo bayan wata ganawar Sirri da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi da Sanata Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso a dai-dai lokacin da tsohon gwamna Ganduje ya je Villa domin kai ƙarar gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf bisa ƙaddamar da rusau da ya yi kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito.
