Connect with us

Labarai

DSS Za Ta Nemi Karin Wa’adin Ci Gaba Da Tsare Emefiele A Gaban Kotu

 

Akwai yiyuwar Rundunar Tsaron ta farin kaya DSS ta garzaya zuwa kotu, a ranar Talata mai zuwa, domin Neman izinin kotu wajen ci gaba da tsare dakataccen gwamnan CBN Godwin Emefele.

DSS na neman Karin wa’adin ci gaba da tsare Emefele ne, har tsawon lokacin da za su kammala yi masa tambayoyi.

Wata majiya a hukumar ta DSS ta shaida wa daya daga cikin wakilanmu cewa, akwai yiyuwar hukumar ‘yan sandan sirri ta garzaya kotu domin samun umarnin ci gaba da tsare shi ba tare da wata matsala ba.

A ranar Juma’a ne shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele daga mukaminsa nan take.

Wannan dai ya biyo bayan binciken da ofishin sa ke yi ne da kuma shirin yin garambawul a bangaren hada-hadar kudi na tattalin arzikin kasar, a cewar wata sanarwa da daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey ya fitar.

A cewar sanarwar, an umurci Emefiele da ya gaggauta mika al’amuran ofishinsa ga mataimakin sa Mista Folashodun Adebisi Shonubi, wanda zai rike mukamin gwamnan babban bankin CBN har sai an kammala bincike da kuma gyaran da ake fatan aiwatarwa.

Jami’an DSS sun kama shugaban bankin da aka dakatar a Legas a ranar Asabar da ta gabata a cikin jirgin sama mai zaman kansa zuwa Abuja.

Wani faifan bidiyo na bidiyo ya nuna shugaban bankin da aka dakatar yana a cikin wata mota kirar Hilux marar lamba tare da rakiyar jami’an tsaro.

Bayan ya sauka daga motar ne aka raka shi cikin wani jirgi inda jami’an tsaro ke jiran tarbarsa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet