Connect with us

Labarai

Sai mun gyara zukatanmu za a samu ingantacciyar Dimukuraɗiyya- Dakta Bugaje

Dr. Usman Bugaje yayin bikin zagayowar ranar dimokuraɗiyya Najeriya wanda cibiyar nazarin harkokin dimokuradiyya da siyasa ta Jami’ar bayero da ke gidan Mumbayya haɗin gwiwa da ƙungiyar Samar da ingantattun shugabannin Arewacin Najeriya da kuma ƙungiyar wayar da kan matasa ta SEDSAC suka shirya a dakin taro na sa’adu Zungur da ke Gidan Mumbayya, ya ce sai an gyara zukata tare da wanzar da zaman lafiya sannan za a samu ingantacciyar Dimukuraɗiyya.

Jaridar Kakakihausa ta ruwaito cewa, taron ya samu halartar manyan bakii kuma masana a fannin siyasa da suka haɗa da Dr.vUsman Bugaje da Dr. Malam Ibrahim Shekarau tsohon Gwamnan jihar Kano, sai Farfesa Hafiz Abubakar tsohon mataimakin gwamnan Kano da sarkin Gaya wanda ya samu wakilcin Dan Dakan Gaya Alhaji Aminu Ibrahim gaya, da kuma Malam Ibrahim Khalil ,sai Farfesa Kamilu Sani Fagge da sauran manyan baƙi

Shugaban kungiyar ta SEDSAC Kwamared Umar Hamisu Ƙofar Na’isa, ya bayyana cewa su na shirya wannan biki ne a duk ranar 12 Janairun kowacce shekara domin wayar da kan matasa masu tasowa musamman abinda ya danganci Dimokuraɗiyya da kuma yadda za a farfaɗo da mutuncin fannin siyasa a fadin Najeriya.

Haka zalika ya kara da cewa wannan taro ya kasance karo na bakwai da suka shirya, ya kuma ji daɗin yadda mutane da manyan baki suka amsa gayyarta domin bada tasu gudunmawar.

A ƙarshe ya yi kira ga matasa da su jajirce wajen yin koyi da abinda magabatan ƴan siyasa na gari suka yi domin kawo sauyi a tsakanin al’ ummar Najeriya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet