Labarai
Cikin Hotuna: Yadda gwamnatin Abba Gida-gida ta rushe Shatale-talen gidan Gwamnati
Gwamnatin jihar kano ƙarƙashin Engr. Abba Kabir Yusuf, ta rushe Shatale-talen Kofar gidan gwamnati.

Gwamnatin ta ƙaddamar da aikin ne cikin daren jiya talata da wata ƙatuwar Katafila.


Kafar yaɗa labarai ta Kadaura, ta ruwaito cewa, sai dai har zuwa safiyar yau babu wani dalili da gwamnatin Kano dangane da rushe Shatale-talen wanda ya kasance mafi kyau a faɗin jihar.
