Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano Za Ta Sake Gina Irin Shataletalan Da Rushe A Wani Wurin Daban

 

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana shirinta na sake gina katafaren shateletalen da ke kusa da gidan gwamnati, wanda a baya ta rushe.

Gwamnati ta yanke shawarar mayar da irin tsohon ginin zuwa wani wurin mai tsaro a tashar jirgin saman Naibawa da ke wajen birnin Kano.

Gwamna Abba Yusuf, a wata ganawa da mai tsara ginin Jubilee na Golden Jubilee, Kaltume Hana, ya tabbatar da sadaukarwar da gwamnati ta yi wajen samar da ababen more rayuwa.

Ya kuma tabbatar wa da ‘yan jihar cewa, an yi nazari a tsanake domin tabbatar da cewa ba za a samu kalubale a sabon wurin da za a mayar ba.

Ya ci gaba da cewa, “Wannan matsugunin ya shaida yadda muka himmatu wajen kiyaye muhimman alamomin al’adu da bunkasa ci gaba a jihar Kano.

“Muna son samar da ingantattun ayyuka ga ‘yan kasarmu.”

Hana wadda ta zana ginin katafaren ginin na Golden Jubilee, ta bayyana godiyarta ga gwamna Abba Yusuf da gwamnatin jihar Kano bisa yadda suka kiyaye aikinta na musamman.

Ta ce, “Ina matukar godiya ga Gwamna Abba K Yusuf da gwamnatin jihar Kano bisa yadda suka gane darajar zane na.

“Abin alfahari ne ganin an kiyaye aikina kuma an ba ni sabo.”

An yanke shawarar mayar da zanen shataletalen ne bayan an yi la’akari da mahimmancinsa na ado da al’adu.

Gwamnati na da burin kiyaye tarihin tsarin da kimar fasaha tare da samar da yanayi mafi aminci kuma mafi dacewa don martaba shi.

“Gwamnatin jihar Kano ta himmatu wajen bunkasa ababen more rayuwa tare da kiyaye dimbin al’adun gargajiyar yankin. Mayar da taswurar da aka yi a shataletalen ya shaida wannan alƙawarin,” wata sanarwa daga Yusuf a daren Lahadi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet