Connect with us

Labarai

Wata Zanga-Zangar Adawa Da Rusau Ta Barke A Jihar Kano

 

Daruruwan masu zanga-zanga a ranar Litinin fin nan sun gudanar da wata zanga-zanga a titunan Kano domin nuna rashin jin dadinsu da yadda gwamnatin jihar ke ci gaba da gudanar da ayyukan rushe-rushe.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnati ta ruguza wasu gine-gine yayin da wasu da dama kuma aka yi wa alamar rugujewar.

Gwamnati ta tsara matakin da ta dauka ne saboda cewa filin an yi gine-ginen ne “ba bisa ka’ida ba” wanda gwamnatin da ta shude ta bayar.

Gine-ginen da tuni aka rusa sun hada da aikin na biliyoyin Naira a tsohon Otel din Daula, da wuraren sayayya a filin Polo da filin Idi, yayin da aka sanyawa wasu gine-ginen gidaje na kasuwanci alamar rushewa da za a rushe a Unguwar Salanta da hanyar BUK.

Yayin da gwamnati ta dage cewa babu gudu babu ja da baya a shirinta na dawo da tsarin raya biranen Kano wanda ya hada da cire gine-ginen da aka gina a wuraren jama’a, masu zanga-zangar da suka mamaye tituna a safiyar ranar Litinin sun bukaci gwamnati ta janye matakin da ta dauka.

Da alluna irinsu “Gwamna Abba K Yusuf, matakinka na janyo korar masu zuba jari”, “Kada ka kawo rashin tsaro a jiharmu, Maigirma Gwamna”, da “ A bari doka ta yi aikinta” da dai sauransu.

Masu zanga-zangar bayan sun taru a otal din Daula da aka rushe, sun zarce zuwa shedkwatar ’yan sanda domin yin rajistar kokensu.

Da yake jawabi a madadin masu zanga-zangar, Kwamared Zahraddeen Sani Baba na kungiyar hadin kan samar da shugabanci na gari da kawo sauyi, ya ce idan har gwamna mai ci yana da wani abu a kan magajinsa, “Don Allah a kira shi ya amsa tambayoyi maimakon hukunta ‘yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba da kuma lalata jarin su.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet