Labarai
Gwamnatin Abba Gida-gida ta dakatar da biyan ma’aikata kusan 11,000 da Ganduje ya ɗauka
Akanta Janar na jihar Kano, Abdulkadir Abdulsalam ne ya bayyana haka a hirarsa da manema labarai.
Ya ce, gwamnan ya dakatar da biyan albashin ne har sai an kammala tantance sababbin ma’aikatan domin gane waɗanda suka cancata da kuma ƴan alfarma.
Ya kuma ce, duk ma’aikatan ƙananan hukumomi da tsohuwa gwamnati ta mayar ma’aikatan jiha a ƙarshen wa’adinta za su ci gaba da karɓar albashinsu na ƙaramar hukuma.
Sai dai ya umarce su da su ci gaba da aiki ma’aikatun da aka tura su na jiha har zuwa lokacin da za a tantance su domin gano makomarsu.
Kafar yaɗa labarai ta Indaranka ta ruwaito cewa, Akanta Janar ɗin ya kuma yi wa ma’aikata da ƴan fensho albishir cewa daga yanzu an daina yanke musu kuɗinsu kamar yadda ya ce ana yi a gwamnatin da ta gabata.
