Labarai
NDLEA ta cafke Wiwi mai nauyin Kilogiram 5,344.1
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA, ta ce, ta cafke Tabar Wiwi da aka shigo da ita mai nauyin kiligiram 5,344.1 a jihar Lagos.
Hukumar ta bayyana hakan a wata sanarwa da jami’inta na hulɗa da jama’a na ƙasa Femi Baba Femi, ya fitar,
Sanarwar ta ce, hukumar ta samu bayanan sirri game da wata babbar mota da ke ɗauke da tabar.
Haka kuma ta ƙara da cewa, nan take jami’an hukumar suka yi wa motar kwanton ɓauna tare da kama buhu 50 na Tabar Wiwi ɗin wadda nauyinta ya kai kilogiram 2,434.1 a kan babbar hanyar Epe zuwa Lekki da ke jihar.
Hukumar ta kuma ce, “Direban motar ya fice daga cikinta, inda ya shiga wata karamar mota ƙirar Hilux da ke yi wa babbar motar tasa rakiya”.
