Labarai
Shugaba Tinubu ya gana da wakilan bankin Amurka a Villa
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya gana da wakilan bankin Amurka a fadar mulkin Najeriya ta Villa da ke Aso Rock a birnin Tarayya Abuja.
Rahotonni sun bayyana cewa shugaban ya jagoranci ganawar ne a yau Talata a ƙoƙarinsa na farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya da ya sha alwashi.
Wakilan bankin na Amurka sun zo ne a ƙarƙashin jagorancin shugaban bankin na yankin Saharar Afirika, Mr Bernard Mensah.
Haka kuma, sauran ƙusoshin bankin na Amurka da suka halarci zaman sun haɗa da shugabar yankin Saharar Afirika, Mrs Yvonne Ike Fasinro da shugaban fannin zuba jari na yankin Saharar Afirika, Mr Chuba Ezenwa.
Sai dai ba a bayyana cikakken bayani kan ganawar tasu ba.
