Connect with us

Labarai

Masarautar Zazzau ta dakatar da guda cikin Hakimanta

Majalisar Masarautar Zazzau, ta sanar da dakatar da Alhaji Mustapha Adamu Ubaidullah daga muƙaminsa na Hakimi kuma Marafan Yamman Zazzau.

A takardar sanarwar da mai magana da yawun masarautar Abdullahi Aliyu Kwarbai ya fitar yau Talata, masarautar ta ce, ta amince cikin gaggawa ta dakatar da Hakimin har sai abin da hali ya yi zuwa nan gaba.

Masarautar ta kuma ce, daukar matakin ya biyo bayan koken da al’ummar Unguwar Magajiya da ke birnin Zariya suka yi na zargin cin zarafin wani mutum da ake yi wa basaraken.

Jaridar Solacebase, ta ruwaito cewa majalisar masarautar ta samu Hakimin da laifin zartar da hukunci kan wani mutum Yusuf Yahaya mazaunin Unguwar Magajiya wanda a bisa doka ba shi da damar yin hakan, a cewar sanarwar.

Masarautar ta kuma yi jan hankali ga dukkan Hakimai da Dagatanta da sauran masu riƙe da sarautar gargajiya cewar ba ta amince da su rika ɗaukar doka a hannunsu ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet